Wasu kwararru daga cibiyar hana yaduwar cutar tarin fuka ta Nijeriya, sun koka da yadda cutar ke yawan kisan mutane a fadin kasar nan.

Shugaban cibiyar Lovett Lawson, ta ce akalla mutane 18 ke mutuwa duk sa’a daya a dalilin kamuwa da cutar.

Lawson ta bayyana haka ne, a wani zama da cibiyar ta yi domin daukar matakan da su ka dace wajen wayar da kan mutane game da cutar a ranar cutar tarin fuka ta duniya.

An dai kebe ranar 24 ga watan Maris domin wayar da kan mutane game da cutar a wani mataki na dakile hanyoyin yaduwar ta.

Lawson ta ce abin takaici ne, yadda duk kokarin da ake yi wajen hana yaduwar cutar, amma har yanzu ta na kara yaduwa inda yanzu haka Nijeriya ta na jerin kasashen Afrika da cutar ta yi wa katutu.

Ta ce rashin ba mutanen da ke dauke da cutar cikakkiyar kulawa, da rashin zuwa asibiti domin yin gwajin cutar na daga cikin matsalolin da ake fama da su.