Shugaban kungiyar likitoci ta Nijeriya reshen jihar Ondo Wale Oke, ya ce tsakanin watannin Janairu zuwa Fabrairu mutane 120 sun kamu da zazzabin Lasa, yayin da 15 su ka mutu sakamakon haka.

Ya ce bincike ya nuna cewa, kananan hukumomin Owo, da Ose, da Akoko ta Arewa, da Akure ta Kudu da ta Arewa na daga cikin garuruwan da ke fama da cutar.

A cikin watan Janairu, ya ce mutane 82 ne su ka kamu da cutar, sannan 15 sun mutu ta dalilin kamuwa da ita.

Ya ce rashin zuwa asibiti da wuri da kuma shan magani ba tare da izinin likita ba na daga cikin matsalolin da su ka sa mutane mutuwa.

Oke ya ce za su bi asibitocin da ke kananan hukumomi domin wayar da kan mutane game da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar, inda a yanzu haka sun kammala da karamar hukumar Akoko.

Leave a Reply