Bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe babban zaben da ya gudana, ya janyo mummunan hargisti da ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane a jihar Legas.
Wata majiya ta ce, rayukan mutane uku sun salwanta, yayin barkewar wani mummunan rikici a yankin Okokomaiko da tsibirin Lagos.
Rayukan wani jami’in ‘yan sanda da wasu ‘yan Tireda biyu sun salwanta, inda a halin yanzu wani jami’i ke cigaba da jinya a gadon asibiti.
Mutane da dama sun samu munanan raunuka daban-daban, yayin rikicin da ya barke sakamakon bayyana nasarar shugaba Buhari.
Lamarin dai ya auku ne, bayan wasu gungun Matasa sun rika shawagin nuna farin ciki game da nasarar da shugaba Buhari ya samu a unguwar Okokomaiko.