Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya ce jam’iyya APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen razana magoya bayan jam’iyyar PDP a kokarin ganin sun lashe zaben da ya gudana ranar Asabar da ta gabata.

Tambuwal ya ce, jam’iyyar APC ta hango faduwa makonni uku kafin zaben, sakamakon haka ne su ka fito da abubuwa da dama yayin gudanar da zaben don ganin sun kai ga nasara.

Gwamnan ya kara da cewa, ba a kai kayan zabe cikin lokaci ba a rumfunan zaben da jam’iyyar PDP ke da matukar karfi ba, an kuma samu matsalar zirga-zirga, wanda hakan ya sa ba a fara zabe cikin lokaci ba.

A zaben dai, jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe kujerun Majalisar Dattawa uku da na Majalisar Wakilai bakwai, yayin da PDP ta samu Majalisar Wakilai biyu, an kuma bayyana zaben kujera daya a matsayin wanda ba a kammala ba a Mazabar Bodinga da Dange-Shuni da Tureta.

Tambuwal, ya yi kira ga magoya bayan sa su fito zaben gwamna da na ‘yan Majalisar Jiha, ya na mai cewa kada jama’a su razana ko su bari a tsoratar da su.