Masu zanga zanga a Algeria sun bukaci mutane su fito a yau Juma’a domin yin zanga-zangar da aba a taba ganin irin ta ba a kasar.

Wadanda suka shirya wannan zanga-zangar na son hana shugaba Abdulaziz Bouteflika ya tsawaita wa’adin mulkin sa ne.

Tun dai watan jiya ne ‘yan kasar suka fara nuna ranshin amincewar su da matakin da shugaban mai shekara 82 da haihuwa ke son dauka.

Wadanda suka kira jama’a su fita titunan kasar suna kiran lamari da taruwar mutane miliyan Ashirin, wanda wani take ne da masu adawa da mulkin Shugaba Bouteflika ke amfani da shi na hana shi sake tsayawa takara bayan ya shafe shekara 20 ya na mulkin kasar.

Wannan matakin ya kara fusata mutanen kasar da ke ganin Mista Bouteflikan ba shi da lafiyar da zai iya sauke nauyin shugaban kasa.

Amma masu neman sauyi a kasar na fuskantar tarjiya daga wadanda ke amfana da mulkin, kuma kawo yanzu hankalin jama’a na kan sojojin kasar wadanda kawo yanzu ba su dauki wani mataki a kai ba.

Leave a Reply