Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO za ta fara amfani da na’ura da ke iya gano cutar shan-inna ga yara.
Na’urar kuma zata iya gano cututtuka kamar su bakon dauro da kwalara da shawara da kuma cuta mai karya garkuwan jiki HIV.
Wasu jami’an hukumar a Korea suka kirkiro wannan na’urar tare da nuna yadda ake amfani da ita ga hukumar lafiya ta WHO a ofishin ta da ke Jamhuriyyar Kongo.
WHO ta bayyana cewa, amfani da na’urar zai taimaka wajen ganin an kawo karshen cutar a kasashen Afrika.
Idan ba a manta ba, bincike ya nuna cewa, kasashen Nijeriya, Afghanistan da Pakistan ne suka rage a duniya da har yanzu su ke fama da cutar shan inna.