Wata kotu a tanzaniya ta yanke wa wani malamin makaranta mai shekara 51 hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kashe wani dalibi mai shekara 14 da ya yi sakamakon dukan sa.

Malamin ya zane dalibin ne tare da dukan sa da wani abu mara kaifi a makarantar su da ke Bukoba a arewa maso yammacin Tanzania a watan Agustan bara, yana mai zargin yaron da satar wata jaka da aka nema aka rasa.

Sperius dai ya musanta zargin, amma duk da haka Malam mai suna Mtazangira sai da ya musguna masa.

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, alkalin babbar kotun kasar Lameck Mlacha ya samu Mtazangira da laifin kisan kai, amma ya wanke wani malamin mai suna Heriet Gerald. °�v�0