Dubban ‘yan Aljeriya sun sake fitar dango a babban birnin kasar Algiers, hadi da wasu biranen, inda suka sabunta zanga-zangar neman shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika, ya yi murabus.
Sabunta zanga-zangar, ya biyo bayan yunkurin shugaba Bouteflika, na kwantar da hankalin ‘yan kasar, ta hanyar janye aniyar neman wa’adi na 5, amma da sharadin soke zaben shugabancin kasar da aka tsara yi a ranar 18 ga watan Afrilu, har zuwa wani lokaci cikin wannan shekara, inda zai sanar da sabon lokaci.
La’akari da cewa matakin ka ‘iya nufin Shugaba Bouteflika, mai shekaru 82 zai iya kara tsawon shekara guda bisa shugabancin, ya sa ‘yan kasar sabunta zanga-zangar tilasta masa yin murabus.