Amurka ta haramtawa wasu jami’an kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC shiga cikin ta, wadanda ke cikin tawagar masu bincikar zarge-zargen da ake yiwa sojinta, na aikata laifukan yaki da cin zarafin dan Adam a Afghanistan da wasu kasashe.
Yayin bayyana daukar matakin, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya kara da cewa a shirye suke, wajen daukar Karin mataki na kakakabawa manyan jami’an kotun ta ICC wasu takunkumai, muddin suka cigaba da kokarin bincikar sojin Amurkan ko na sauran kasashen da suke kawance, bisa zargin aikata laifukan yaki.
Haramtawa jami’an kotun duniyar ta ICC takardar Visa, shi ne Matakin farko da Amurka ta dauka kan kotun, bayan barzanar yin hakan da ta yi a watan Satumba na shekarar bara.
A watan Nuwamban shekarar 2017, babbar mai gabatar da kara ta kotun ICC, Fatou Bensouda, ta nemi izinin soma bincikar zargin sojojin Amurka da aikata laifukan yaki a Afghanistan.