A Jamhuriyar Nijar ,hukumomin sun gano wani nauyin allurar hana kamuwa da cutar sankarau na jabu da yanzu haka ake samu a wasu wurraren sayar da magunguna a Birnin Yameh.

Ministan kiwo lafiya, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ya na mai kira ga jami’an kiwon lafiya su yi hatara tareda kira ga al’umma don ganin sun tseguntawa jami’an tsaro irin wurraren da ake sayar da wadanan allurai na jabu. Ranar alhamis ne a yayin wani bincike daga jami’an kiwon lafiya na birnin Yameh, a wanin shagon sayar da magunguna suka tayar da wannan launin allura, wanda ake zaton shine ya haddasa mutuwar mutane kusan 500 a shekara ta 2015 da wasu 200 a shekara ta 2017 a lokacin da cutar ta kunno kai a wasu sassan kasar.