Pic 21 Scene of a collapsed 3 storey building under construction at Sogoye, Bode Area of Ibadan on Friday (15/3/2019) 02219/16/3/2019/Timothy Adeogodiran/ICE/NAN Pic 22. Scene of a collapsed 3 storey building under construction at Sogoye, Bode Area of Ibadan on Friday (15/3/2019) 02220/16/3/2019/Timothy Adeogodiran/ICE/NAN Pic 23. One of the survivors of the collapsed 3 storey building under construction at Sogoye, Bode Area of Ibadan on Friday (15/3/2019) 02221/16/3/2019/Timothy Adeogodiran/ICE/NAN

Gwamnatin jihar Legas ta fara rusa gine-ginen da aka sanya wa alamar rushewa a unguwar Ita-Faaji da ke jihar.

Wannan na zuwa ne bayan wani bene mai hawa uku ya rufta a jihar a ranar Laraba.

Rahotanni sun ce gwamnatin jihar ta mika wa masu gidajen takardun gargadi kafin ta fara rushe su tun a ranar Juma’a.

Akalla mutum 11 aka rasa, yayin da aka ceto 50 da ransu bayan da benen mai hawa uku ya rufta.

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar ta kammala aikin ceton a wajen da ginin ya rufta.

Ana ganin zai yi wuya a san takamaiman yawan mutanen da ke cikin ginin a lokacin da abun ya faru, saboda gini ne mai dauke da gidajen mutane da kuma makarantar da ke da dalibai kusan 100.

Makarantar na hawa na uku, sannan gidajen mutane ne a hawa na tsakiya sai kuma shaguna da ke kasa.

Mazauna yankin sun ce baya ga ginin da ya rushe, akwai wasu gidajen da aka yi musu alamar cewa a rusa su amma sai masu su suka goge fentin alamar da gwamnati ta saka.