Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce ba zai taya shugaba Muhammadu Buhari murnar lashe zabe ba, saboda kura-kuran da ya ce an tafka yayin gudanar da zaben.

Atiku, ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben da Hukumar zabe ta fitar, wanda ya bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya yi nasara da gagarumin rinjaye.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Atiku ya ce in da a ce ya fadi ne a sahihin zabe, da tuni ya kira wanda ya yi nasara cikin kankanen lokaci da samun labarin nasarar sa domin taya shi murna.

Atiku Abubakar ya kara da cewa, bai taba ganin tabarbarewar dimokradiya a cikin shekaru 30 na fafutukar sa kamar yadda ta faru a zaben ranar Asabar da ta gabata ba.

Leave a Reply