Hukumar zabe mai zaman kan ta INEC, ta gudanar da wata ganawa domin sake duba zaben Shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

Ganawar dai ta zo ne sa’o’i kadan bayan zaben, tsakanin tawagar hukumar zaben da kwamishinonin zabe.

Shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce za a sake duba ga tsarin da kuma matakan da aka bi sannan a yi gyara inda bukatar hakan ta taso.

Ya ce ganawar za ta taimaka wajen kammala tsare-tsaren zaben gwamnoni da ke zuwa a jihohi 29 a fadin Nijeriya.

Leave a Reply