Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a JAMB, ta a shekara ta 2019 dalibai miliyan 1 da dubu 800 ne su ka yi rajistar rubuta jarabawar.

Daraktan yada labarai na hukumar Fabian Benjamin ya sanar da haka, yayin da ya ke ganawa da manema labarai a Legas, inda ya ce hukumar ta rufe yin rajista da sayen fom tun a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Sai dai ya ce wadanda su ka sayi fom kafin ranar 21 ga watan Fabrairu, za su iya yin rajistar jarabawar daga lokacin zuwa karfe 12 na daren ranar 25 ga watan Fabrairu.

Benjamin, ya kuma karyata rade-radin da wasu ke yi cewa an fara buga takardar shiga rubuta jarabawar, ya na mai cewa wannan labarin ba gaskiya ba ne, domin babu yadda za a iya buga takardar ba tare da hukumar ta tsaida ranar rubuta jarabawa ba.

A karshe ya yi kira ga mutane su kwantar da hankalin su, cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta sanar da ranar rubuta jarabawar.