Fadar shugabn kasa ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba zai sa baki a wajen zaben shugaban majalisa ba.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kan harkokin majalisa Ita Enang, ya bayyana haka, inda ya ce, Buharin ba zai sa baki bane saboda ya bayar da dama ga ‘yan majalisar su zabi wanda suke so su zaba domin jagorantar majalisar.

Ya ce, shugaban kasa ya yi imani da cewa, a ba kowa ‘yancin sa wanda doka ta ba shi, saboda haka zai kyale ‘yan majalisar su zabi wanda suke so ya zama shugaban su.

In za a iya tunawa dai a ranar Alhamis ne zababbun sanatoci suka ce jam’iyyar APC ce za ta shege gaba wajen zaben shugaban majalisa domin tabbatar da cewa ba a samu rabuwar kai a jama’iyyar sakamakon zaben ba.

Enang, ya ce, shugaban kasa zai goyi bayan dukkan wanda ‘yan majalisar suka zaba, ya ce, daga cikin tsarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi ne ya ba kowa damar da tsarin mulki ya ba shi.

Saboda haka Buhari ba zai taba yin azarbabi ba, sai ya roki ‘yan majalisar da su zabi wanda ya cancanta.