Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce za ta ci gaba da tattara sakamakon zabe na mazabu da rumfunan zabe a jihar Bauchi domin hada sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.
Hukumar tace ta nada sabon jami’in zabe da zai ci gaba da tattara sakamakon, wanda kuma zai maye gurbin tsohuwar jami’ar tattara sakamakon wacce ta janye daga aikin saboda barazana da tace tana fuskanta.
A makon jiya ne hukmar zaben ta INEC ta bayyana cewa zaben jihar Bauchi bai kammala ba, kuma za a sake zabe a karamar hukumar Tafawa Balewa, saboda rashin samun sakamakon zaben kamar yadda dokokin zabe suka tanada, bayan tashin hankali yayin tattara sakamakon.
INEC ta ce za ta yi amfani da kwafin takardun da aka rubuta sakamakon zaben a mazabu, wadanda daga nan za a samu sakamakon karamar hukumar.
Ta ce ta gano cewa akwai kurakurai wajen lissafin kuri’un da aka soke a rumfuna hudu a karamar hukumar Ningi inda aka ce sun kai 25,330, maimakon 2,533 wadanda INEC ta ce su ne alkaluma na gaskiya.
Hukumar ta ce a yanzu za a sake lissafi da alkaluma na gaskiya na kuri’un da aka soke a karamar hukumar Ningi da suka kai 2,533.rֳ���A