Dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce duk da ba su gamsu da matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dauka na sake zabuka a wasu yankuna na wasu jihohi  ba, a shirye su ke su shiga a fafata da su a zaben da a sake a wasu yankuna na jihar a ranar 23 ga watan Maris, 2019.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce, rashin gaskiya da adalci ne yasa aka ki amincewa da sakamakon zaben da aka yi na ranar 9 ga watan Maris.

Ya ce hukumar zabe ba ta yi amfani da dokar zabe a jihar Ogun ba, da ta ce ya zama wajibi a sake zaben a wasu wurare idan aka samu yawan kuri’un da aka soke sun zarta ratar dake tsakanin ‘yan takara 2 dake kan gaba.

Jagoran jam’iyyar ta PDP a jihar Kano ya ce, bisa la’akari da yadda suka ga abubuwa na tafiya a wannan zabe da za a sake a wasu wurare a jihar, to za su dauki mataki domin kuwa za su tabbatar da cewa dukkanin akwatunan da za a jefa kuri’a a cikin su ko da sau 100 za a jefa, to dan takarar su ne zai samu nasara.