Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jajantawa iyalan wadanda aka rasa rayukan su a sanadiyyar ruftawar wani bene a jihar Legas.

Dalibai ne dai da dama suka mutu, yayin da ginin ya rufto a kansu.

Shugaba Buhari, ya yi fatar Allah ya kara wa iyalan wadanda aka rasa a iftila’in, sai ya tabbatar da aniyar su ta daukar mataki.