Uwargidar Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, ta ziyarci wadanda ginin Ita-Faji ya rufta masu a birnin Lagas a babbar asibitin jihar domin yi masu jaje.

Uwargidar shugan kasar ta mika jajen ta ga wadanda lamarin ya ritsa da su, wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 20, ciki harda yaran makaranta.

Aisha, wacce ta dauki lokaci wajen ziyartan bangaren mata da kananan yara a asibitin, ta yi addu’ar Allah ya ba iyalan wadanda suka mutu juriya da hakuri.

Ta kuma yiwa wadanda ke kwance a asibiti addu’ar samun lafiya.

Daya daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu kuma malama a makarantar benen da ya rufto, Easter Samuel, ta nuna alhini kan lamarin.

Malamar mai shekara 19, wacce ke samun kulawa a asibitin tayi addu’ar Allah ya kare ta daga sake fuskantar wannan lamari a rayuwar ta.

Shugaban likitocin asibitin, Gani Kale, ya ce yara 10 aka kwantar a asibitin bayan faruwar lamarin.

Aisha ta samu rakiyan tsohon jigon Lagas a mulkin soji, ritaya Birgediya Janar Buba Marwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Plateau, Pauline Tallen da sauransu.

Leave a Reply