Kotun koli na tarayya ta jadada hukuncin da babban kotun jihar Legas ta yanke na bayar da umurnin kwace kudi Naira Biliyan 2 da dubu 400 daga hannun Patience Jonathan, uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Wannan na zuwa ne kwanaki takwas bayan kotun kolin da tabbatar da hukuncin da babban kotun ta bayar na amincewa da bukatar gwamnatin tarayya na kwace kudi Dala Miliyan 8 da dubu 4 da ake kyautata zaton na matar tsohon shugban kasar ne.

Kotun kolin ta kuma umurci Patience ta koma babban kotun na Legas domin tayi bayanin dalilin da ya sa ba ta mika kudin zuwa ga gwamnatin tarayya ba.

A hukuncin da alkalai biyar suka yanke a a ranar Juma’a, Kotun koli tayi watsi da daukaka karar da wani kamfanin da EFCC ta gano cewa na Patience Jonathan ne mai suna Lawari Funiture and Bath Limited, da aka gano ba shi da nagarta.

Babban lauya Mike Ozekhome ne ya daukaka karar sai dai EFCC ta ce akwai kudade da yawa a kamfanin da ake zargin na haramun ne.Sai dai a hukuncin da aka karanta a madadin Amiru Sanusi da bai samu halartan kotun ba, kotun koli ta ce ba ta ga dalilin da zai sa ta tayi katsalandan cikin abubuwan da sauran kotunan biyu suka gano ba.

Leave a Reply