Yar’uwar Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Oyinkansola Saraki ta kalubalanci dan uwanta a wani shirin talbijin, inda tace ya gaza tunanin jama’a a lokacin da ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar Kwara.

Oyinkansola, ta soki kokarin dan uwanta sannan ta roki mutanen Kwara yafiya yayinda ta bayyana a shirin kafar TVC a ranar Alhamis.

Shugaban majalisar dattawa ya kasance zababben gwamnan Kwara a 2003, bayan kammala mulkin sa, yaki bin umurnin mahaifin sa na tallafa yar’uwar sa, Gbemisola tsohuwar Sanata domin ta gaje shi.

 Maimakon haka sai ya marawa gwamna mai mulki, Ahmed Abdulfatah, baya inda ya kayar da yar’uwar ta sa.

Shugaban majalisar dattawan ya samu cikasa a lamarin siyasar sa a zaben 2019, bayan gaza samun nasarar komawa majalisar, wanda dan takarar jam’iyyar APC, Ibrahim Oloriegbe, ya doke shi, dan takarar gwamnan da ya daura Razak Atunwa, ma ya sha kaye a hannun dan takarar APC, Abdurahman Abdurazaq, wanda hakan ya dukufar da mambarin siyasar Sarakin baki daya.

Da take martini kan lamarin, Oyinkansola tace dan uwan nata ya bata kunya matuka kan yadda ya jagoranci jihar.