Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Karkashin jam’iyyar PDP
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Karkashin jam’iyyar PDP

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya mika godiyar sa ga miliyoyin ‘yan Nijeriya sakamakon fitar farin dango da su ka yi wajen kada kuri’ar su.

Atiku, ya bayyana haka ne ta bakin mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Phrank Shaibu, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa, jam’iyyar PDP na dakon sakamakon zaben da aka tattara ta na’urar da ta tanada domin duba sakamkon zaben da ya gudana a fadin Nijeriya.

Atiku Abubakar, ya ce ‘yan Nijeriya su kara hakuri nan da dan lokaci kadan mafarkin su da suka dade suna jira zai tabbata.