Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kasa rashen jihar Gombe ta gayyaci shugaban karamar hukumar Dukku tare da kansilolin yakin bisa zargin laifin sayen kuri’u a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar.
Mai Magana da yawun hukumar zabe na jihar Mallam Bello Bajoga, ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Gombe.
Bajoga, ya ce ganin irin abubuwa da suka faru a baya, hukumar ta bukaci duk wanda ya samu labarin inda ake sayan kuri’a ko dillancin su ko kuma bada toshiyar baki ya tsegunta mata domin daukar matakin da ya dace.
Ya kara da cewa, ana cikin gudanar da zabe ne aka kira jami’an hukumar EFCC aka shaida masu cewa, wasu na siyan kuri’u, wanda hakan ya sa jami’an ba su yi kasa a gwiwa ba wajen isa inda ake aikata wannan haramtaccen aiki.
Mallam Bello, ya ce tuni suka kama kansilan da ake zargin da bada kudi kana sun gayyaci shugaban karamar Dukku domin gudanar da bincike a kan alakar su da kuma rawar da suka taka a wannan aiki.