Dan Takarar Gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo Adebayo Adelabu ya sha kasa a hannun takwaran sa na jam’iyyar PDP Seyi Makinde a zaben Gwamna da ‘yan majalisun dokoki na jihohi da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Injiniya Seyi Makinde na PDP ya samu kuri’u dubu dari 515 da dari 621 yayin da Adebayo Adelabu na jam’iyyar APC ya sam kuri’u dubu dari 357 da dari 982.