Dan takarar gwamnan jihar Zamfara na jam’iyyar APC Alhaji Mukhtar Shehu ya lashe zaben da ya gudana a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.

Baturen zabe na jihar Farfesa Kabiru Bala na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya ce Mukhtar Shehu ya samu kuri’u dubu 534 da 541.

Sai kuma babban abokin karawar san a jam’iyyar PDP Dakta Bello Matawallen Maradun da ya samu kuri’u dubu 189 da 452.

Leave a Reply