BOKOWasu ‘yan kunar bakin wake da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun yi kokarin kai hari a wani Cocin Katolika da ke birnin Shawu  a jihar Adamawa.

Kamar yadda rahotanni da mazauna yankin ke cewa, wasu ‘yan kunar bakin wake sun yi shigar burtu da zummar shiga cocin, sai dai kafin su karasa sai Bom din da ke jikin su ya tashi, wanda nan take biyu suka mutu, yayin da aka ce na ukun su ya ranta a na kare kamar yadda wani dan yankin ya tabbatar wa manema labarai.

Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta jihar ba ta yi karin haske a kan lamarinba, sai dai kakakin rundunar tsaro ta Civil Deffence Suleiman Baba ya yi karin haske game da abin da ya faru da halin da ake ciki.

Lamarin dai ya na zuwa ne, yayin da ake ci-gaba da tattara sakamakon zaben gwamna da na majalisun dokoki na jihar.

Leave a Reply