Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta saki mataimakin gwamnan jihar Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinan kananan hukumomi Nasiru Sule Garo.

An dai kama manyan jami’an gwamnatin biyu ne, bayan sun yi kutse tare da kawo hayaniya a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamna a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

Ana zargin mataimakin gwamnan da kwamishinan da yaga takardun sakamakon karamar hukumar, wanda ake jira domin kammala tattara sakamakon zaben kujerar gwamna a matakin jiha.

Jihar Kano dai ta na da kananan hukumomi 44, kuma tuni sakamako daga kananan hukumomi 43 sun shiga hannun baturen zabe na jihar in banda na karamar hukumar Nasarawa. /\”] 07��1�