Jami’an tsaro sun kama jami’in tattara sakamakon zabe Kelechi Ezirim na Karamar Hukumar Ohaji Egbema ta jihar Imo, tare da jami’in Kula da ayyukan Zabe na karamar mai suna Chris Ogbuadu.
An dai kama jami’an ne, jim kadan bayan sun gabatar da sakamakon zaben gwamna daga karamar hukumar su, wanda wasu jam’iyyu su ka yi korafi a kan sa.
Dukkan jami’an biyu sun amsa laifin sun gabatar da sakamakon zabe na bogi a inda ba a gudanar da zabe ba.
Ezirim, ya ce ya na sane da cewa wasu ‘yan jagaliya sun kwace kayan zabe na wasu rumfuna, amma duk da haka ya amince da sakamakon da aka ba shi daga wadannan yankuna da ba a yi zaben ba.