Dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya samu izinin gudanar da bincike a kan kayayyakin da hukumar zabe ta yi amfani da su a zaben ranar 23 ga watan Fabrairun na shekara ta 2019.
Bisa hukuncin da mai shari’a A.H Suleiman na kotun daukaka kara ya yanke, Sanata Shehu Sani zai gudanar da bincike a kan kayayyakin da hukumar zabe ta yi amfani da su.
Umarnin kotun dai, ya biyo bayan korafin da Sanatan ya shigar, a yunkurin sa na ci-gaba da kalubalantar sakamakon zaben da ya gudana makonni kadan da su ka gabata.
A cikin korafin da Shehu Sani ya shigar, ya nemi Kotu ta tursasa wa hukumar zabe ba shi damar gudanar da bincike a kan wasu muhimman kayayyakin zabe da su ka hadar da takardun sakamakon zabe.
Sanata Shehu Sani dai ya na kalubalantar sakamakon zaben da hukumar ta kaddamar da Uba Sanin a jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a shiyyar Kaduna ta Tsakiya.