Kungiyar masu kamfanonin kere-kere da ababen masarrufi ta Nijeriya MAN, ta gargadi gwamnatin tarayya akan kudurin ta na kara harajin samar da kayayyaki.

Shugaban kungiyar na kasa Segun Ajayi Kadir ya yi wannan gargadi, a lokacin da ya ke maida martani game da kudurin gwamnati da hukumar tara kudaden haraji ta kasa na kara kudaden harajin.

Ya ce ko kusa wannan kudurin na gwamnati ba zai yi wa masu sana’ar samar da abubuwa da ma kananan ‘yan tireda da ke hada-hadar saida su har zuwa talakawan da ke amfani da kayayyakin masarufi dadi ba.

Haka kuma, ya bukaci gwamnati ta dubi duminiyar ‘yan Nijeriya ta hanyar janye wannnan kuduri domin maslahar kowa da kowa.

Idan dai za a iya tunawa, hukumar tara kudaden haraji ta kasa,  ta bukaci ‘yan Nijeriya su kwana da shirin ko-ta-kwana na karin harajin kayayyaki a shekara ta 2019.