Dan takarar gwamnan jihar Nasarawa na jam’iyyar APGA Labaran Maku, ya ki amincewa da sakamakon zaben da ya gudana ranar Asabar 9 ga watan Maris a kan abin da ya kira damfara da magudi.

Labaran Maku ya bayyana haka ne a kauyen Wakama da ke Nasarawa Eggon, yayin da ya ke tsokaci a kan sakamakon da hukumar zabe ta sanar a ranar Litinin da ta gabata.

A cewar sa, an tafka magudi da kura-kurai, wanda hukumar zabe tare da hadin gwiwar jami’an tsaro su ka yi hadaka wajen aikatawa.

Maku ya ce jam’iyyar APGA ta ki amincewa da sakamakon zaben ne, saboda ganin cewa bai haska gaskiyar kuri’un da jama’a su ka kada ba.