Rundunar sojin Nijeriya, ta ce ta kama mutane 24 masu alaka da sace akwatunan zabe da garkuwa da mutane a jihohin Abia da Imo da Rivers.
Kakakin rundunar soji Sagir Musa ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce sun kama mutane 15 daga cikin mutane 24 a jihar Abia.
Ya ce daga cikin mutane 15 da su ka kama, biyar ‘yan jagaliya ne da ‘yan siyasa ke amfani da su domin tada rikici a lokacin zabe.
Musa ya ce, dakarun sojoji sun kama wasu mutane shida a hanyar Osisioma dauke da takardun zaben da aka riga aka dangwale.
Haka kuma, ya ce sojojin sun kama wasu masu garkuwa da mutane da su ka sace wani ma’aikacin hukumar zabe.
A karshe ya ce sojoji sun ceto wani mutum mai suna Authur Nkama a karamar hukumar Odukpani, wanda aka yi garkuwa da shi a Ikot ta jihar Rivres. d[val�07#o1