Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta fitar da sunayen zababbun ‘yan majalisun tarayya, sai dai akwai kujerun majalisar tarayya 20 da har yau ba a bayyana ba saboda rashin kammaluwar zabe.

Daga cikin kujerun majalisar wakilai 360, jam’iyyar APC ta na da 211, yayin da jam’iyyar PDP ke da 111.

Sauran jam’iyyu da za su samar da ‘yan majalisar tarayya sun hada da APGA mai ‘yan majalisa shida, jam’iyyar ADC kuma ta na uku, sai kuma jam’iyyar AA mai guda biyu, yayin da jam’iyyar PRP ita ma ke da biyu, sai kuma jam’iyyun ADP da APM da SDP da kowaccen su ke da wakili daya.

Daga cikin zababbun ‘yan majalisar dai, akwai mata 10 daga cikin 300 da aka sanar da samun nasarar su.

Leave a Reply