Ana fargabar mutuwar mutane da dama, bayan wani kazamin hari da wasu gungun ‘yan bindiga su ka kai a wani kauye da ke cikin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

‘Yan bindigar dai sun afka wa kauyen Bargaja da ke cikin karamar hukumar Batsari ne a kan babura da dama a ranar Talatar nan, inda su ka bude wa jama’a wuta.

Wani shaidun gani da ido ya tabbatar wa manema labarai cewa, ya ga akalla gawarwakin mutane uku zuwa shida bayan tafiyar ryan bindigar, yayin da shanu da dama sun bace, wanda ake zargin maharan ne su ka yi awon gaba da su.

Sai dai kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina game da batun ya ci tura, sakamakon kakakin rundunar SP Gambo Isa bai amsa tambayar neman karin bayani da manema labaru su ka yi masa ba.