Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta bayyana zaben kujerar Gwamnan jihar Kano a matsayin wanda bai kammala ba.

Shugaban hukumar zaben na jihar Kano Farfesa Bello Shehu ya sanar da halin da ake ciki a kan zaben da yammacin ranar Litinin da ta gabata.

Farfesa Shehu, ya ce sakamakon da su ka tattara ya nuna cewa, dan takarar jam’iyyar PDP Abba Yusuf ya samu kuri’u miliyan 1, da dubu 14, da 474, yayin da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ya samu kuri’u dubu 987 da 819.

Ya ce an samu tazarar kuri’u dubu 26 da 655 tsakanin Abba da Ganduje, sai dai yawan kuri’un da aka soke a kananan hukumomi 22 ya kai dubu 141, da 694, wanda ya sa dole a sake zaben a wuraren da aka soke, domin yawan su zai iya tasiri wajen tabbatar da nasarar wanda ke kan gaba ko sauya sakamakon zaben.