Dubban Jama’a a jihar Rivers, sun gudanar da zanga-zangar adawa da matakin dakatar da tattara sakamakon zaben Gwamna da hukumar zabe ta yi, wanda ke zuwa bayan rikice-rikice da zargin magudin zabe a wasu mazabun jihar.

Matakin dakatar da tattara sakamakon zaben dai, ya zo ne bayan a ranar Lahadin da ta gabata wasu gungun mutane sanye da kayan soji dauke da makamai sun yi wa cibiyar tattara sakamakon zaben kawanya, tare da neman hukumar zabe ta dakatar da aikin ta, wanda daga bisani rundunar sojin Nijeriya ta ce ba jami’an ta ba ne.

A Jihar Rivers dai, dubban magoya bayan jam’iyyar APC are da kungiyoyin fararen hula ne su ka gudanar da zanga-zangar domin adawa da matakin dakatar da zaben.

Tuni dai gwamnan jihar Nyesome Wike ya zargi hukumar zabe da jami’an tsaro da kuma Jam’iyyar APC da yunkurin juya sakamakon zaben.