Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fara raba kayayyakin zabe a daukacin kananan hukumomi 44 da ke Jihar Kano.
Mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Garba Lawal ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya a Kano.
Lawal ya ce ma’aikatan hukumar INEC sun fara tantance kayayyakin zabe musamman takardun kada kuri’a a kowace karamar hukuma tun a ranar Larabar da ta gabata.
A jihar Kaduna kuwa, Hukumar INEC ta ce ta kai kayayyaki zabe a dukkan kananan hukumomi 23 da ke jihar, domin zaben gwamna da na majalisar dokokin jihar.
Babban Jami’in yada labarai da hulda da Jama’a na INEC a jihar Kaduna, Sani Abdulfatah ya bayyana haka ga kamfanin dillanci labaran Nijeriya da ke Kaduna.
Abdulfatah ya ce an rigaya an ware kuma an tantance dukkan kayan aikin zaben na kananan hukumomin jihar 23, wadanda za a yi zabe da su a mazabu 255 da kuma rumfunan zabe 5,102 da ke fadin jihar.