Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta Nijeriya “JAMB” ta tsayar da ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar rubuta jarabawar gwaji wato Mock Examinations a turance.

Hukumar ta ce ta shirya wannan jarabawa ne domin dalibai su koyi amfani da na’uran komfuta da kuma yadda tambayoyin jarabawar za su kasance.

Jami’in hukumar Fabiyan Benjamin ya sanar da haka a ranar Talatar da ta gabata,  inda ya kara da cewa dalibai za su iya fara buga takardar da zata ba su  damar shiga dakin rubuta jarabawar daga ranar 6 ga watan Maris.

Benjamin ya ce, har yanzu hukumar ba ta tsayar da ranar rubuta ainihin jarabawar ba, amma wata majiya ta tabbatar da cewa za a rubuta jarabawar ne a ranar 16 ga watan Afrilu.

Idan ba a manta ba, hukumar JAMB ta fara siyar da fom din jarabawar ne tun a ranar 10 ga watan Janairu, sannan ta rufe siyar da fom din ranar 21 ga watan Fabrairu.

Leave a Reply