Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa “NCDC” ta bayyana cewa, an samu karuwar yawan mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon kamuwa da cutar zazzabin lassa a Nijeriya.

Hukumar ta ce karuwar masu fama da cutar da kuma wadanda suka mutu ya faru ne a tsakanin watannin Janairu zuwa Maris.

Bincike ya nyna cewa, hukumar ta yi wa mutane miliyan 3 da dubu 1 da dari 374 gwajin cutar, sai dai mutane 420 daga cikin su sun kamu da cutar, sannan mutane 93 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar.

An samu barkewar cutar ne a kananan hukumomi 66 da ke jihohi 21 da suka hada da Edo da Ondo da Bauchi da Nasarawa, Ebonyi da Plateau da Taraba da Abuja da Adamawa da Gombe.

Sauran sun hada da Kaduna da Kwara da Benue da Rivers, Kogi da Enugu da Imo da Delta da Oyo da Kebbi da Cross River.

Bincike ya nuna cewa an samu karin mutane 39 da suka kamu da cutar a wasu jihohi 6, sai dai ba a samu wani ma’aikacin kiwon lafiya da ya kamu da cutar ba.

Idan ba a manta ba, tun da cutar ta bullo a wannan shekarar ma’aikatan kiwon lafiya 15 ne suka kamu da cutar.