Akalla mutane 113  ne suka rasa rayukan su a jihar Zamfara tun bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da ya nuna shugaba Muhammadu Buhari  ne ya yi nasara.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, mahara da masu garkuwa da mutane sun lalata gidaje da kona dukiya mai dimbin yawa a jihar, lamarin da ya sa mazauna kauyukan Shinkafi da Anka da Tsafe suka tsere daga garuruwan su.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Asabar din da ta gabata, ‘yan sanda a jihar Zamfara sun tabbatar da kashe mutane 29 a Karamar Hukumar Shinkafi, sannan kuma aka kashe wasu 30 a kauyen Kware da ke jihar.

Wani mazaunin yankin mai suna Bala Shinkafi, ya ce mahara su na tafiya ne a cikin jerin gwanon Babura, kowane dauke da goyon dan bindiga daya, kuma yawan su kimanin 100.

Kakakin Operation Sharan Daji, Clement Abiade ya tabbatar da kisan mutanen, amma bai fadi adadin su ba.

A halin yanzu dai, al’umomin yankin sai kauracewa su ke daga kauyukan su sakamakon harin ‘yan bindiga da su ke fuskanta.