Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta hana mutane da sauran masu ababen hawa zirga-zirga a garuruwan birnin da kewaye.
Mai Magana da yawun rundunar Anjuguri Mamzah ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya rabawa manema labarai a Alhamis din da ta gabata.
Mamzah ya ce an hana zirga-zirga ne daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma, sai dai ya kara da cewa, an sahale wa motocin daukar marasa lafiya na asibitoci da motocin Hukumar Kashe gobara da wasu masu gudanar da ayyuka na musamman cigaba da gudanar da ayyukan su bisa daluri.
Anjuguri Mamzah ya ba daukacin al’ummar birnin hakuri sakamakon takura su da ka yi na rashin gudanr da harkokin su da suka saba na yau da kulllum. �������Qư���