Majalisar dinkin duniya ta ware 8 ga watan Maris ta kowacce shekara a matsayin ranar mata ta duniya.

Taken bikin ma bana shine, dai-dai-ta gudunmawar maza da mata ga cigaban kasa, amma har yanzu ana korafi a kan yadda  aka yi wa mata nisa a fannoni da dama na rayuwa.

Sai dai a lokacin da ake gudanar da wannan biki na bana, sakamakon zaben majalisar dokoki na tarayya da aka yi a watan Fabrairu ya nuna cewa mata 6 ne kacal su ka yi nasara a cikin kujeru majalisar dattawa 109, yayin da 11 kuma su ka yi nasara a kujerun majalisar wakilai 360.

Tuni dai wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin mata suka fara bayyana da muwar su a kan sakamakon zaben.

Wasu kasashen duniya sun dauki haramin yin bukukuwa da zanga-zanga da kuma taruka al’barkacin wannan rana ta mata ta Duniya.

A kasar Philippines daruruwan mata sun cika tituna a birnin Manila, tare da bayyana rashin jin dadin yadda shugaba Rodrigo Duterte ya maida batun yi wa mata fyade tamkar abun barkwanci.

A Brazil ma kusan irin hakan ce za ta kasance, inda dubban mata suka shirya wani taro da za su maida martani a kan wasu kalaman batanci da shugaba Jair Bolsonaro ya yi a kan matan.