Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ba da tabbacin gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki a ranar Asabar 9 ga watan a dukkan fadin Najeriya.

Hukumar ta kara da cewa za a tabbatar da amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a, a dukkan mazabun da za a gudanar da zaben a jihohi 29.

Jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Festus Okoye ya ce duk rumfar da ‘yan bangar siyasa su ka hana jami’an zabe amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a, ba za a kidaya kuri’un ta ba.

Shugaban hukumar zaben Mahmud Yakubu, ya ce hukumar ta buga takardun kada kuri’a miliyan dari hudu da ashirin da daya, wanda ya zo daidai da yawan masu rijista a runfunan zabe dake fadin Najeriya.