Firai ministan Habasha Abiy Ahmed ya taimaka wajen sasanta shugabannin kasashen Somaliya da Kenya.
Kenya da Somaliya sun mayar da dangantakar diflomasiya bayan wata matsala kan mallakar wasu rijiyoyin mai da ke cikin teku.
Firai ministan Habasha Abiy Ahmed ne ya shiga tsakani, inda shugabannin Somaliyan da Kenya suka gana da juna kai tsaye kan batun a Nairobi.
A watan da ya gabata ne Kenya ta kori jakadan Somaliya daga kasarta bayan da rahotanni suka fito cewa Somaliyar na sayar da wasu daga cikin rijiyoyin man da ke yankin da suka dade suna takaddama a kai.
Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ne ya karbi bakuncin takwaransa na Somaliya Mohamed Farmajo a Nairobi, domin samar da mafita kan mallakin yankin gabar tekun Indiya da masana suka ce yana da albarkatun man fetur da gas mai tarin yawa.