Kotu ta umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ba dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar damar isa ga takardun da hukumar ta yi amfani da su a zaben da ya gabata, wanda hakan zai ba shi damar shirya shigar da kara dangane da sakamakon zaben.
Hukuncin kotun mai alkalai uku, ya umurci hukumar zaben ta ba Atiku ko kuma wakilansa damar isa ga takardun da aka yi amfani da su a kowace rumfar zabe.
Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar ba wani kamfanin kwararru mai zaman kansa damar isa ga kayayyakin zaben kamar yadda dan takaran na PDP ya bukata.
Atiku
ya yi watsi da sakamakon zaben da ya ba shugaba Muhammadu Buhari nasara, tare
da zargin yi masa magudi, yayin da jam’iyyar APC ta ce, a shirye take ta kare
kanta a gaban kotu.