Rahotanni sun ce yanzu haka ana kawo sakamakon zaben da aka sake a runfunar zabe 36 a jihar Bauchi, sai dai kuma babban jimi’in tattara sakamakon zaben a jihar Farfesa Muhammad Kyari, bai baro jihar Adamawa zuwa Bauchi ba.

Kwamishinan zaben jihar Ibrahim Abdullahi, ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai da masu sanya ido jawabi a shelkwatar hukumar dake Bauchi.

Ibrahim Abdullahi, ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa hukumar na kulle-kullen murde sakamakon zaben gwamnan a jihar ne.

Ya ce dukkannin jami’an tattara sakamakon zaben na kananan hukumomi 15 da aka sake zaben sun iso cibiyar domin mika sakamakon  su, sai ya danganta rashin fara aikin ga rashin zuwan babban jami’in Farfesa Muhammad Kyari.