Dakarun Syria da Amurka sun ce daular ISIS mai shekaru biyar ta zo karshe, bayan da aka dakushe mayakanta a kasar Syria.
Mayakan sun yi ta daga tutoci a Baghuz, gari na karshe da masu ikirarin jihadin ke rike da iko, a lokacin da take kan ganiyarta, kungiyar IS na da iko a kan fadin kilomita 88,000 a fadin Syria da Iraki.
Sai dai duk da kwace iko daga kungiyar, ana tunanin tana ci gaba da zama babbar barazana ga tsaron duniya.
Shugaba Trump ya ya jinkirta janye dakarun Amurka daga Syria
Har yanzu IS na nan a yankin kuma tana da rassa a kasashe da dama kamar Najeriya da Yemen da Afghanistan da kuma Philippines.
Rundunar hadin gwiwa da Kurdawa ke jagoranta ta fara yakinta na karshe da kungiyar IS ne a farkon watan Maris, inda sauran mayakan suka boye a kauyen Baghuz a gabashin Syria.
An tilasta wa hadin gwiwar rage bude wuta bayan da aka gano cewa akwai dimbin fararen hula a garin, zaune a gidaje, rumfuna da wasu maboya a karkashin kasa.