jihar Filato Simon Bako Lalong, na jam’iyyar APC ya Gwamnan lashe zaben gwamnan jihar bayan sake zaben a wasu mazabu dake jihar.
Nasarar tasa ta zo ne bayan zaben da aka sake a runfunar zabe 40 daga cikin kananan hukumomi 9 inda Simon Lalong, ya samu kuri’a dubu 12 da 327, shi kuma Jeremiah Useni, na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a dubu 8 da 487.
Da yake bayyana wanda ya lashe zaben babban jami’in tattara sakamakon zabe na jihar Filato Farfesa Richard Anande Kimber, ya ce a zaben na shekarar 2019, Simon Lalong ya samu kuri’a dubu 595 da 582, wanda ya doke babban abokin karawar sa Jeremiah Useni, da ya samu kuri’a dubu 546 da 813.