Shelkwatar sojojin Najeriya ta kafa wani kwamitin bincike karkashin jagorancin Manjo Janar T.A. Gagariga, don binciko zarge-zargen da ake yi wa sojin lokacin zaben 2019.

Kwamitin wanda keda Wakilai hafsoshi tara zai binciki irin rawar da sojojin suka taka ko wani abu da suka yi da ya sabawa ka’idoji da sharuddan aiki ya yin zaben da aka kammala.

Tuni dai kwamitin ya tattaro bayanai daga wadanda keda korafi don tantance sahihancin da akewa dakarun ciki har da zargin yunkurin kisan gilla ga gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike.

Kwamitin kazalika zai binciki kashe wani Hafsa mai mukamin Laftanar da raunata wani Hafsa da wasu sojoji ya yin zaben Gwamna a jihar.

Gwamnan jihar Rivers wanda ya yi bayani ga yan kwamitin ya yi korafi kan shishshigin da yake zargin soji sunyi a jihar sa ya yin zaben al’amarin da ya bayyana ko kadan bai cancanta ba.

Wani masanin kimiyyar siyasa Farfesa Jibrin Ibrahim wanda ke zama wakili a cibiyar raya demokradiyya ta CDD, ya ce lalle kan bincike abune mai kyau, amma da bai kamata ace soji ne zasu gudanar da shi ba duba da yadda suma ake zargin su.