Jami’an tsaro sun kama shugaban kafar yada labarai ta AIT Raymond Dokpesi a babbar tashar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, jim kadan bayan dawowar sa daga birnin Dubai domin duba lafiyar sa.

Kafar Talabijin ta AIT ne ta sanar da haka, inda ta kara da cewa wani jami’in hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, ya ce umurni ne suka samu daga sama na cewa su kama shi da zarar ya dawo gida Nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, Raymond Dokpesi na fuskantar tuhume-tuhume ne daga hukumar hana zambar kudi da karya tattalin arzikin kasa EFCC a kan zargin hadin baki da wasu wajen karkatar da kudaden da aka ware domin siyen makamai, wanda yawan ya  kai Naira miliyan dubu biyu wanda ake zargin ya amsa daga ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro Sambo Dasuki.